short Hausa Novel

HATTARA MATA

Wata matar aure ce tayi tunanin cewa bari ta gwada mijinta ta gani idan ta fita bada izinin shi ba wane mataki zai dauka?

Sai ta samu biro da takarda ta rubuta kamar haka:

"Na gaji da zama dakai gaskiya na tafi gidan mu Allah ya hada kowa da rabonsa"
 
Bayan ta gama rubutawa saita ajiye takardar a kan tebur, ita kuma ta shiga karkashin gado ta boye.
<script async src="https://pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js?client=ca-pub-3064461154629178"
     crossorigin="anonymous"></script>
<ins class="adsbygoogle"
     style="display:block; text-align:center;"
     data-ad-layout="in-article"
     data-ad-format="fluid"
     data-ad-client="ca-pub-3064461154629178"
     data-ad-slot="9738889725"></ins>
<script>
     (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
</script>
 
Da mijin ya dawo sai ya duba bai ga matarshi ba, can sai hankalin shi ya kai kan takardar data ajiye kan tebur, ya dauka ya karanta, sai yayi murmushi, ya zauna kan kujera yayi hamdala, ya zaro wayarshi daga aljihu yayi kira  yace" Baby na yau ina da labari me dadi, soyayyarmu ta samu cigaba, na dawo wannan sakarar matar tawa wai ta tafi gidansu, saboda haka mun huta da kama hotal, kishirya yau a gidana zamu kwana"
<script async src="https://pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js?client=ca-pub-3064461154629178"
     crossorigin="anonymous"></script>
<ins class="adsbygoogle"
     style="display:block; text-align:center;"
     data-ad-layout="in-article"
     data-ad-format="fluid"
     data-ad-client="ca-pub-3064461154629178"
     data-ad-slot="9738889725"></ins>
<script>
     (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
</script>

Bayan ya gama wayar ya dauko biro shima yayi rubutu a jikin takardar ya fice daga gidan

Matar tashi ta fara zubar da  hawaye daga inda take a boye, data tabbatar ya fita daga gidan saita fito idanunta jawur zuciyarta cike da kunci da kuma dana sanin me yasa tayi abinda tayi?
<script async src="https://pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js?client=ca-pub-3064461154629178"
     crossorigin="anonymous"></script>
<ins class="adsbygoogle"
     style="display:block; text-align:center;"
     data-ad-layout="in-article"
     data-ad-format="fluid"
     data-ad-client="ca-pub-3064461154629178"
     data-ad-slot="9738889725"></ins>
<script>
     (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
</script>

Ta kai hannu ta dauko takardar da shima mijin nata yayi rubutu, ta karanta sakon daya rubuta kamar haka "Baki iya ßuya ba, kin bar kafarki ta leko waje, ina shigowa na ganki, na manta ban siyo biredin da zamu sha shayi bane, ina zuwa"

Popular posts from this blog

Short Hausa Novel

LABARINA SEASON 8 EPISODE 9

GAWUNA YA YANKE JIKI YA FADI BAYAN GANAWARSU DA TINUBU